Lagos Ta Horar da Sama da Mutum 500 Kan Sana’o’i; A Lokaci Guda Wasu Jihohin Arewa Na Gudanar da Shirye-shiryen Auren Gata
Daga Wakiliya
Yayin da wasu jihohin Arewa ke gudanar da shirye-shiryen auren Zawararawa ko auren gata domin tallafa wa masu buƙata, Gwamnatin Jihar Lagos ta mayar da hankali kan ƙarfafa matasa da masu sana’o’i ta hanyar horas da su kan dabarun dogaro da kai.
Gwamnatin jihar ta horas tare da bai wa sama da mutum 500 da suka haɗa da matasa, manoma da masu ƙananan sana’o’i tallafi a wani shirin koyar da sana’o’i da Cibiyar Raya Karkara (CERUD) ta shirya a sassa biyar na jihar.
An kammala zagayen ƙarshe na shirin ne a Ikorodu West LCDA, inda Mai Bai Wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu Shawara kan Raya Karkara, Dr. Nurudeen Yekini Agbaje, ya ce shirin na daga cikin matakan gwamnatin jihar na rage talauci da bunƙasa tattalin arzikin al’umma.
Ya bayyana cewa an horas da mahalarta kan kiwon kifi, yin burodi da kayan zaki, girbin zuma, da kuma ƙera kayayyakin amfani na gida ta hanyar amfani da sinadarai.
A cewarsa, sama da mutum 500 ne suka amfana kai tsaye da kuma a kaikaice, inda aka ba su kayan aiki da ƙwarewar da za su taimaka musu su dogara da kansu tare da samar da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.
Sakatariyar Dindindin ta Ma’aikatar Kananan Hukumomi, Harkokin Sarauta da Raya Karkara ta jihar, Mrs. Kikelomo Bolarinwa, ta yabawa Gwamna Babajide Sanwo-Olu bisa ci gaba da tallafa wa matasa da mazauna karkara, tare da ƙarfafa mahalarta su yi amfani da damar da suka samu domin cimma ‘yancin cin gashin kai ta fuskar tattalin arziki.
Shi ma Shugaban Ikorodu West LCDA, Sulaimon Kazeem Olarewaju, ya ce irin waɗannan shirye-shiryen sun taimaka wa mutane da dama wajen kafa sana’o’i masu ɗorewa tare da rage ƙaura daga karkara zuwa birane.
A madadin waɗanda suka amfana, Mrs. Ajibola-Ogunde Anuoluwapo ta gode wa gwamnatin jihar Lagos bisa horaswa da kayan aikin da aka ba su, tana mai cewa hakan zai taimaka musu wajen inganta rayuwarsu da samun dogaro da kai.




