Duk wanda ya ce bai amfana da tallafin Tinubu ba, to baya Najeriya – Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu 

Daga Wakiliya

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ce duk wani dan Najeriya da ya ce bai amfana da tallafin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba, to yana zaune ne a wajen Najeriya.

Ahmed Aliyu ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar da shirye-shiryen tallafawa ’yan Najeriya, musamman marasa galihu, inda ya ambaci tallafin abinci, takin zamani kyauta da sauran tallafi.

“Idan ba ka ga tasirin ayyukan Tinubu ga ’yan Najeriya ba, to ba ka Najeriya,” in ji gwamnan.

Ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a Jos, yayin wani taron karawa juna sani na kasa da kungiyar JIBWIS ta shirya kan siyasa da hadin kan kasa.

Ahmed Aliyu ya yi watsi da ikirarin ’yan adawa cewa gwamnatin Tinubu ba ta yi wani tasiri ba cikin shekaru uku, yana mai cewa irin wadannan kalamai farfaganda ne.

Gwamnan ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su sake zaben Bola Tinubu a 2027, yana mai cewa yana da yakinin shugaban zai ci gaba da kawo sauyi a kasar.

Taron ya samu halartar Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin.

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Tinubu za ta dawo da binciken mai a Arewa bayan tsaida aikin tun bayan hawansa mulki 

Shugaban RMAFC ya kuma ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na damuwa da yadda aikin ya tsaya, yana mai cewa an ba gwamnonin Bauchi da Gombe tabbacin cewa za a sake tura kayan aiki da ma'aikata domin ci gaba da aikin.

Murna Ta Koma Ciki: Tinubu ya janye sunayen kwamitin yakin neman zaɓensa na 2027 da APC ta fitar ya sa a sake gyare-gyare

Yanzu dai ana sa ran sabon jerin kwamitin zai ƙara wakiltar sassa daban-daban na jam’iyyar tare da shigar da manyan jiga-jiganta kafin fara babban yaƙin neman zaɓen 2027.

Maza ba wawaye bane: Ba za ki yi wa mijinki rashin kunya sannan ki sa ran zai ci gaba da sonki ba – Zainab

Jamiu Zainab ta ce wasu mata ba sa son a yi musu gyara, kuma kan yi gardama ko mayar da magana idan mazajensu suka yi magana da su.

Zan yi aiki tukuru don ganin Tinubu ya zarce a 2027 –  Christopher Musa ya karɓi naɗin da APC ta yi masa

Janar Christopher Musa ya kuma yi kira ga ’yan jam’iyyar APC da sauran ’yan Najeriya masu kishin ƙasa da su kasance cikin haɗin kai, yana mai cewa yana da yakinin APC za ta yi nasara a zaɓen 2027 tare da ci gaba da inganta shugabanci da tsaro a ƙasar.

Tinubu Zai Ci Zabe Kuma APC za ta ci gaba da mulkar Najeriya har bayan 2031 -inji Yari 

Yari ya ce duk da kalubalen da gwamnatin Tinubu ke fuskanta, yana ganin ayyukan gwamnatin cikin shekaru uku da suka gabata za su taimaka wa APC wajen samun ƙarin wa’adi.

Kanun Labarai

Kamfanin Dangote ya faɗaɗa kai man fetur kyauta zuwa Kano da wasu jihohi domin saukar da farashin man a gidajen mai

Ana sa ran rage kuɗin safarar man fetur zai ba ‘yan kasuwa ƙarin damar sauke farashin man a gidajen mai, idan aka samu ci gaba da rage kuɗaɗen da ke cikin tsarin rarraba man.

Maido da Tallafin Man Fetur (Subsidy) zai mayar da Najeriya baya, ya jefa mutane a wahala – Idris

Sai dai ya amince cewa ‘yan Najeriya na fuskantar wahalhalu sakamakon sauye-sauyen, amma ya ce dawo da tallafin man fetur ba mafita ba ce.

Wani Magidanci ya nemi Kotu ta raba aurensa da matarsa saboda tana zuba ruwa kan gadon idan ya nemi saduwa da ita

Alkalin kotun, Chief Ademola Odunade, ya ce bayan duba lamarin, ya amince da bukatar Dauda tare da rusa auren nasu.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img