Gwamnatin Tinubu za ta dawo da binciken mai a Arewa bayan tsaida aikin tun bayan hawansa mulki 

Gwamnatin Tinubu za ta dawo da binciken mai a Arewa bayan tsaida aikin tun bayan hawansa mulki

Daga Wakiliya

Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen farfaɗo da aikin binciken man fetur a filin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe, bayan aikin ya tsaya.

Shugaban Hukumar Rabon Asusun Tarayya da Hukumar Kula da Kasafin Kuɗi ta Jihohi (RMAFC), Muhammad Bello, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin ziyarar tantance aikin a Bauchi.

Muhammad Bello ya ce farfaɗo da aikin na da muhimmanci ga ci gaban Arewa maso Gabas da kuma tattalin arzikin Najeriya.

Ya ce RMAFC za ta duba matakan da suka dace domin dawo da aikin, tare da miƙa rahoton bincikenta ga hukumomin da abin ya shafa.

Shugaban RMAFC ya kuma ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na damuwa da yadda aikin ya tsaya, yana mai cewa an ba gwamnonin Bauchi da Gombe tabbacin cewa za a sake tura kayan aiki da ma'aikata domin ci gaba da aikin.

A nasa bangaren, Kwamishinan Albarkatun Ƙasa na Jihar Bauchi, Maiwada Bello, ya ce aikin binciken ya tsaya ne kusan watan Yulin 2025, bayan al'ummar yankin suka lura cewa kamfanin da ke gudanar da aikin ya fara kwashe kayansa.

Ya ce gwamnatin jihar Bauchi a ƙarƙashin Gwamna Bala Mohammed a shirye take ta samar da ma'aikata da sauran tallafin da ake bukata domin ganin an dawo da aikin.

Muhammad Bello ya kuma ziyarci Kwalejin Mai da Iskar Gas ta Bauchi, inda ya yaba wa gwamnatin jihar kan kafa cibiyar horas da ma'aikata da za su iya taka muhimmiyar rawa idan aikin Kolmani ya koma cikakken aiki.

DA DUMI-DUMI

Duk wanda ya ce bai amfana da tallafin Tinubu ba, to baya Najeriya – Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu 

Gwamnan ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su sake zaben Bola Tinubu a 2027, yana mai cewa yana da yakinin shugaban zai ci gaba da kawo sauyi a kasar.

Murna Ta Koma Ciki: Tinubu ya janye sunayen kwamitin yakin neman zaɓensa na 2027 da APC ta fitar ya sa a sake gyare-gyare

Yanzu dai ana sa ran sabon jerin kwamitin zai ƙara wakiltar sassa daban-daban na jam’iyyar tare da shigar da manyan jiga-jiganta kafin fara babban yaƙin neman zaɓen 2027.

Maza ba wawaye bane: Ba za ki yi wa mijinki rashin kunya sannan ki sa ran zai ci gaba da sonki ba – Zainab

Jamiu Zainab ta ce wasu mata ba sa son a yi musu gyara, kuma kan yi gardama ko mayar da magana idan mazajensu suka yi magana da su.

Zan yi aiki tukuru don ganin Tinubu ya zarce a 2027 –  Christopher Musa ya karɓi naɗin da APC ta yi masa

Janar Christopher Musa ya kuma yi kira ga ’yan jam’iyyar APC da sauran ’yan Najeriya masu kishin ƙasa da su kasance cikin haɗin kai, yana mai cewa yana da yakinin APC za ta yi nasara a zaɓen 2027 tare da ci gaba da inganta shugabanci da tsaro a ƙasar.

Tinubu Zai Ci Zabe Kuma APC za ta ci gaba da mulkar Najeriya har bayan 2031 -inji Yari 

Yari ya ce duk da kalubalen da gwamnatin Tinubu ke fuskanta, yana ganin ayyukan gwamnatin cikin shekaru uku da suka gabata za su taimaka wa APC wajen samun ƙarin wa’adi.

Kanun Labarai

Kamfanin Dangote ya faɗaɗa kai man fetur kyauta zuwa Kano da wasu jihohi domin saukar da farashin man a gidajen mai

Ana sa ran rage kuɗin safarar man fetur zai ba ‘yan kasuwa ƙarin damar sauke farashin man a gidajen mai, idan aka samu ci gaba da rage kuɗaɗen da ke cikin tsarin rarraba man.

Maido da Tallafin Man Fetur (Subsidy) zai mayar da Najeriya baya, ya jefa mutane a wahala – Idris

Sai dai ya amince cewa ‘yan Najeriya na fuskantar wahalhalu sakamakon sauye-sauyen, amma ya ce dawo da tallafin man fetur ba mafita ba ce.

Wani Magidanci ya nemi Kotu ta raba aurensa da matarsa saboda tana zuba ruwa kan gadon idan ya nemi saduwa da ita

Alkalin kotun, Chief Ademola Odunade, ya ce bayan duba lamarin, ya amince da bukatar Dauda tare da rusa auren nasu.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img