An Hana Shi Ƙarin Matsayi Bayan Abokinsa Ya Shiga Imel Ya Goge Takardar Promotion ɗinsa
Daga Wakiliya
Wani mutum ya bayyana yadda ya rasa ƙarin matsayi (promotion) a wurin aikinsa bayan abokinsa na kut-da-kut ya shiga imel ɗinsa ya goge saƙon da ke ɗauke da takardar ƙarin matsayin.
A wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, mutumin ya ce abin ya faru ne saboda amincewar da yake yi wa abokin nasa, wanda yake da damar shiga ofishinsa, amfani da kwamfutarsa har ma da shiga imel É—insa ba tare da ya hana shi ba.
Ya ce bayan kamfanin ya aiko masa da takardar ƙarin matsayi ta imel, bai taɓa ganin saƙon ba duk da cewa yana duba imel ɗinsa a kullum. Daga baya wasu daga cikin shugabanninsa da ke ƙasashen waje suka kira shi cikin mamaki, suna tambayarsa dalilin da ya sa bai amsa saƙon ba ko kuma ya bi umarnin da ke tattare da shi.
Mutumin ya ce ya yi ta ƙoƙarin bayyana musu cewa bai ga wani irin saƙo ba, amma a wurinsu sun ɗauka cewa ya yi watsi da damar da aka ba shi. Hakan ya sa aka rufe batun, kuma ya rasa ƙarin matsayin.
Ya ce daga baya, lokacin da ɗaya daga cikin shugabanninsa ya zo Najeriya, ya roƙe shi ya nuna masa saƙon. Bayan ya tabbatar cewa an aika imel ɗin kuma ya isa akwatin saƙonsa, sai ya fara zargin akwai abin da ya faru.
Da ya koma wurin aikinsa, ya nemi a binciki hotunan CCTV na ranar da aka aiko imel ɗin. A cewarsa, binciken ya nuna cewa abokin nasa ne ya shiga kwamfutarsa tare da goge saƙon daga imel ɗinsa.
Ya ce lokacin da ya tambayi abokin nasa dalilin yin hakan, ya amsa cewa shi ne ya goge saÆ™on, amma bai bayar da wani gamsasshen bayani ba, sai dai ya riÆ™a cewa “sharrin shaidan ne.”
Mutumin ya ce abin da ya fi ba shi mamaki shi ne kasancewar ya dade yana taimaka wa wannan abokin, kuma ko da ya samu ƙarin matsayin, shi ma zai amfana ta wata hanya.
A ƙarshe, ya ce ya yafe masa, amma ya sanar da shi cewa daga wannan lokaci dangantakarsu za ta tsaya ne a kan harkokin aiki kawai, ba za su ƙara hulɗar ƙawance kamar da ba.
Bidiyon da mutumin ya ba da labarin ya yaÉ—u sosai a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama ke tofa albarkacin bakinsu kan muhimmancin taka-tsantsan ko da da na kusa.




